Ambaliyar ruwa ta fi muni a Jigawa da Legas – Gwamnati

100

Hukumar kula da ayyukan ruwa ta kasa ta yi kira ga jihohi da kananan hukumomi da su kara kaimi wajen dakile annobar da masifun da suka shafi ambaliyar ruwa a yankunansu.

Hukumar ta ce kiran ya zama dole saboda kasar na kololuwar lokacin ambaliyar ruwa har zuwa farkon watan Oktoba.

Da yake jawabi ga manema labarai jiya a Abuja, babban daraktan hukumar, Clement Nze, ya bayyana jihar Jigawa a matsayin jihar da ta fi fama da matsalar ambaliyar ruwa, inda ya bayyana cewa kimanin kananan hukumomi 16 ne lamarin ya shafa tare da asarar rayuka sama da 50 da asarar dukiyoyi da ababen more rayuwa.

A cewarsa, Legas ce ta biyu da kananan hukumomi 14 kuma an samu asarar rayuka da dama, ida ya kara da cewa sauran jihohin da ambaliyar ta shafa sun hada da Nasarawa, Anambra, Imo, Abia, da sauransu.

Ya yi nuni da cewa, kusan dukkanin abubuwan da suka faru na ambaliya sun faru ne sakamakon cikar koguna da rashin magudanan ruwa da mamakon ruwan sama wanda ya haifar da ambaliya a birane da kauyuka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

6 − four =