Sarkin Ingila Charles na III ya yi magana akan mutuwar Sarauniya Elizabeth

53

Sabon Sarkin Ingila, Charles na uku, ya bayyana rasuwar mahaifiyarsa Sarauniyar Elizabeth ta biyu, wacce ya kira da mahaifiyarsa abar kaunarsa, a matsayin abu mafi bakin ciki da ya faru ga iyalansu.

Daya daga cikin abubuwan farko da sabon sarkin ya gudanar shine furta jimaminsa tare da bayyana yadda mutane ke girmama da kaunar marigayiyar.

Kalamansa na zuwa ne bayan fadar Buckingham ta tabbatar da cewa Sarauniyar Elizabeth ta biyu, wacce tafi kowa dadewa kan karagar mulkin Birtaniya, ta mutu salin alin jiya da rana a Balmoral bayan kwashe sama da shekaru 70 akan karagar mulki.

Da take jawabi ga ‘yan kasar daga fadar gwamnati dake titin Downing, Fira-Ministar Birtaniya, Liz Truss, ta sanar da sabon mukamin sabon sarkin, Charles na uku.

Ana sa ran sabon sarkin, Charles na uku, zai yi jawabi ga ‘yan kasa tare da jagorantar sakonnin ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 − twelve =