Mutane 10 sun mutu sanadiyyar ambaliya a Bauchi

73

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutane 10 sakamakon ambaliyar ruwa da ta lalata gidaje da gonaki da dama a fadin jihar.

Daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga na hukumar, Adams Nayola, ya tabbatar da hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa a yau a Bauchi.

Ya ce lamarin ya tilastawa mazauna yankin neman mafaka a wasu wurare.

Sai dai, Daraktan ya ce hukumar na ci gaba da tattara bayanai kan filayen noma da gidajen da suka lalce a fadin jihar.

Ya ce ambaliyar ta katse hanyoyin wasu kauyukan a kananan hukumomin Jama’are da Misau, inda ya kara da cewa ambaliyar baya-bayannan ta faru ne a karamar hukumar Zaki.

Ya ce hukumar na yin duk mai yiwuwa don samar da kayan agaji ga mutanen da abin ya shafa duk da cewa ana ci gaba da tantance lamarin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 + thirteen =