Liz Truss ta zama Firayi Ministar Biritaniya bayan ganawa da Sarauniya Elizabeth, wacce ta umarceta ta kafa sabuwar gwamnati.
Liz Truss, mai shekaru 47, ta hau kan karagar mulki a yau a bikin da aka tsara tare da sarauniyar, kwana daya bayan da jam’iyyar Conservative mai mulki ta sanar da cewa an zabe ta a matsayin shugabar jam’iyyar.
Wanda ya gabace ta, Boris Johnson, ya sauka a hukumance a lokacin da yayi tasa ganawar da sarauniyar a gidanta na Balmoral a Scotland.
A jawabinsa na karshe a matsayinsa na Firayim Minista, Boris Johnson ya ce manufofinsa sun baiwa kasar karfin tattalin arziki domin taimakawa mutane shawo kan matsalar makamashi.
A jiya, mambobi dubu 172 na jam’iyyar Conservative ne suka zabi Liz Truss domin jagorantar jam’iyyarsu.
Da take magana da mambobin jam’iyyar Conservative a jiya, Liz Truss ta yi alkawarin kawo cigaba a tattalin arziki, da shawo kan matsalar makamashi da kuma tsarin kiwon lafiya, kodayake ba ta da cikakkun bayanai kan manufofinta ba.