Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayar da tallafin kudi naira miliyan 50 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Jigawa.
Ya sanar da bayar da tallafin ne a lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar a fadar gwamnati dake Dutse babban birnin jihar.
Bola Tinubu ya ce ya je jihar Jigawa ne domin jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar musamman wadanda iftila’in ya shafa da wadanda suka rasa ‘yan uwansu da dukiyoyinsu.
Ya bayyana cewa, iftila’in ambaliyar ruwa daga Allah Ta’ala ne kuma ya bayar da gudunmawr kudin ne domin kawai ya rage wa wadanda abin ya shafa wahalhalun da suke fustanta, ba wai ya biya su diyya ba.
Da yake mayar da martani, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya godewa dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar mai mulki bisa ziyarar da ya kai jihar Jigawa da kuma gudunmawar kudaden da ya bayar.