Akalla gawarwakin mutane 15 ne aka gano a kogin Ngadabul da ya yi ambaliya a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Kodinetan hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA na yankin Arewa maso Gabas, Muhammad Usman, ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin.
Da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa jiya a Maiduguri, Muhammad Usman ya ce ana ci gaba da samun karuwar mutanen da suka nutse a kogin da ya shafi al’ummomi da dama da ke zaune a gabarsa a Maiduguri.
Ya kuma bukaci iyaye da masu kula da ‘ya’ya da su fadakar da ‘ya’yansu kan yin wanka a cikin kogin don guje wa nutsewa.
Muhammad Usman ya ce abubuwan da suka faru na ambaliya a yankin Arewa maso Gabas na da matukar tayar da hankali.
A halin da ake ciki kuma, rundunar tsaro ta farin kaya civil defense ta jihar Borno ta tura jami’anta zuwa bakin kogin domin korar yaran dake zuwa wanka a kogin.