Badaru ya soki yajin aikin ASUU a jami’ar Sule Lamido

115

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya ce malaman jami’o’i a karkashin kungiyar ASUU ba su da wasu dalilai da zai sa su ci gaba yajin aikin.

Gwamna Badaru Abubakar ya bayyana haka ne a lokacin wata ganawa da manyan sakatarori, da daraktoci, da mataimakan daraktoci, da shugabannin ma’aikatu da na hukumomin gwamnati a dakin taro na Sir Ahmadu Bello dake Dutse.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan yajin aikin da kungiyar ASUU reshen jami’ar Sule Lamido ta Kafin-Hausa a jihar Jigawa ke cigaba da yi.

Ya bayyana cewa malaman kungiyar ASUU a jami’a mallakar gwamnatin jiha ba ta da dalilin ci gaba da yajin aikin.

Gwamna Badaru Abubakar ya bukaci kungiyar da ta yaba da jajircewar gwamnati kada a yi amfani da ita a rikicin da bai shafe su ba.

A saboda haka ya bukaci dattawa da sauran masu ruwa da tsaki a jihar su shiga tsakani a yajin aikin da ake yi.

A wani labarin mai alaka da wannan, mataimakin shugaban jami’ar Sule Lamido dake Kafin-Hausa a jihar Jigawa, Farfesa Lawan Sani Taura, ya bayyana yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’in ASUU reshen jami’ar ke yi a matsayin marar ma’ana.

Da yake magana a wata tattaunawa ta musamman da gidan rediyon Jigawa, mataimakin shugaban jami’ar ya bayyana cewa yajin aikin abinda takaici ne da ba za a amince da shi ba.

Ya ce ya gana da malaman jama’ar da wadanda basa koyarwa, inda ya sanar da su cewa goyon bayan da suka bawa kungiyoyin ASUU da NASU na kasa na tsawon watanni biyu ya isa, don haka su koma bakin aiki domin amfanin gwamnati da al’ummar jihar Jigawa.

Lawan Sani Taura ya ce ma’aikatan da basa koyarwa sun amince su koma bakin aikinsu amma malaman sun yi kunnen uwar shegu kan bukatarsa.

Mataimakin shugaban jami’ar ya yi kira ga shugaban jami’ar da ya kara himma wajen ganin an kawo karshen yajin aikin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 − 9 =