Amurka: Yan majalisa na shirin tsige Trump

65
Donald Trump

A wani abun da ba’a saba gani ba, majalisar Amurka na yunkurin tsige shugan kasar Donald Trump kan wasu kalamai da yayi lokacin da yake zantawa da shugaban kasar Ukraine ta wayar tangaraho.

Ana dai zargin Trump ne da tursasawa don a basa bayanan sirri kan abokan hamayyarsa na siyasa, wanda ace war mista Adam Schiff wanda shine shugaban kwamitin da ke sa ido kan bayanan sirri da tsaro na Amurka, hakan bai da ce ba, kuma ka iya sa Trump ya rasa kujerarsa na shugaban Amurka.

Schiff ya kara da cewa matukar ya tabbata Trump yana matsawa wani shugaban kasa don bashi bayanan sirri akan abokan hamayyarsa, to babu abinda zai hanasu daukar hukunci da ta dace wanda shine tsige Trump daga mulkin kasar.

A halin yanzu dai, Adam Schiff naci gaba da matsawa fadar gwamnatin white house da ta saki cikakken tattaunawar tsakanin Trump da Volodmir na Ukraine.

Hunter Biden

Shugaban Amurka naci gaba da hurama Volodmir wuta kan sai ya sake gudanar da sahihin bincike kan Hunter Biden, wanda da ne ga Joe Biden, kuma ya na sahun gaba wajen masu neman takarar shugaban kasa a jma’iyar Democrat.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 + two =