Ma’aikatan wutar lantarki za su tafi yajin aiki gobe

97

Matukar ba a samu wani sauyi ba, ma’aikatan wutar lantarkin Najeriya karkashin inuwar kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa za su fara yajin aikin sai baba-ta-gani a gobe kan batutuwan da suka shafi kwadago tsakaninsu da kamfanin watsa wutar lantarki na kasa TCN.

Wata takardar da ke dauke da sa hannun babban sakataren kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa, Joe Ajaero a jiya, ta umurci manyan mataimakan manyan sakatarori da sakatarorin tsare-tsare na kungiyar na shiyya-shiyya da su tabbatar da shiga yajin aikin.

Sanarwar ta kuma umurci ma’aikatan da su yi dafifi a gaban hedikwatar kamfanin watsa wutar lantarki na kasa TCN, yau a Abuja.

Yajin aikin zai kara jefa kasarnan cikin matsalar samar da wutar lantarki.

A ranar 20 ga watan Yuli, tsarin wutar lantarki kasa ya ruguje, lamarin da ya jefa sassa da dama na kasarnan cikin rashin wutar lantarki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × two =