Tarraya Turai ta bayar da tallafin kudi domin ambaliyar ruwa a Najeriya

41

Tarayyar Turai, EU, ta bayar da Yuro dubu 70, kwatankwacin Naira miliyan 30, a matsayin tallafin gaggawa na rage illar ambaliyar ruwa a kasarnan.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau kuma ta mika wa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa a Abuja.

An ba da tallafin ne da nufin tallafa wa kungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya domin kara karfinta da kuma shirye-shiryenta wajen rage illar ambaliyar ruwa a jihohin Ondo, Kogi, Kebbi, Anambra, da Cross River.

Tarayyar Turai ta kara hakan na nuna wajibcin zama cikin shiri a hasashen da aka yi na samun annobar ambaliyar ruwa.

A saboda haka ta ce kungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya za ta dauki matakan riga-kafi don shiryawa hasashen cewa annobar za ta iya haifar da yanayin jin kai kafin lokacin ambaliyar ruwa ta afkawa kasar.

Kungiyar Tarayyar Turai da kasashe mambobinta ne ke kan gaba wajen bayar da agajin jin kai a duniya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × 4 =