INEC ta yi hasashen ‘yan Najeriya miliyan 95 za su kada kuri’a a zaben 2023

51

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a jiya ta yi hasashen samun masu kada kuri’a kimanin miliyan 95 a zaben 2023 a kasarnan.

Shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a wani horon da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bawa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a kan harkokin tsaro a Abuja a gabanin babban zaben 2023.

Mahmad Yakubu ya ce adadin ya haura jumillar masu kada kuri’a na sauran kasashe 14 na yammacin Afirka da miliyan 20.

Ya ce shirye-shiryen zabe, aikawa da jami’an tsaro da aiwatar da zabe sun kasance mafi girman abubuwan da ka iya faruwa a kasa, ko a lokacin zaman lafiya ko lokacin yaki.

Shugaban na INEC ya ce tabbatar da tsaro da tsaron masu kada kuri’a, da na ma’aikatan zabe da kayayyakin zabe, da ’yan takara, da wakilan jam’iyya, da masu sa ido, da kafafen yada labarai da masu sufuri shi ne abu mafi muhimmanci.

A halin da ake ciki, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ce sama da katunan zabe na dindindin gudu duba 389 ne har yanzu ba a kammala karba ba a jihar Kano.

Kwamishinan Zabe na INEC na jihar, Riskuwa Shehu ne ya bayyana haka a lokacin da kwamishinan hukumar korafe-korafen jama’a na tarayya Ahmad Dadinkowa ya kai masa ziyara jiya a Kano.

Riskuwa Shehu wanda sakataren hukumar INEC na jihar, Garba Lawan ya wakilta, ya bayyana cewa, katunan zaben na dindindin wadanda aka yi ne daga shekarar 2011 zuwa 2018.

Kwamishinan zaben ya bayyana cewa an yi rijistar sabbin masu kada kuri’a dubu 569 da 103 a jihar a ci gaba da rijistar masu kada kuri’a da aka kammala.

Riskuwa Shehu ya bukaci masu ruwa da tsaki da su taimaka wa hukumar wajen wayar da kan jama’a zuwa karbar katin zabe na dindindin.

Ya ce za a ci gaba da yin rijistar masu kada kuri’a bayan zaben 2023.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 − 16 =