Za ayi aiki da doka ba sani ba sabo a zaben 2023 – INEC

36

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, za ta aiwatar da dokoki ba sani ba sabo, ba tare da tsoro ko son kai ba, musamman dokar zabe ta 2022, domin tabbatar da sahihin zabe mai cike da gaskiya da amana a zaben 2023.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka jiya a Abuja, a wajen taron tunawa da marigayi Darakta Janar na Cibiyar Zabe ta Kasa, Farfesa Abubakar Momoh, wanda ya rasu a ranar 29 ga Mayun, 2017.

Mahmud Yakubu ya samu wakilcin Farfesa Abdullahi Zuru, kwamishinan hukumar kuma shugaban hukumar zabe ta kasa.

Mahmud Yakubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa hukumar INEC ba ta da wata jam’iyya ko dan takara, amma za ta tabbatar da cewa an kirga dukkan kuri’u masu inganci sannan masu kada kuri’a ne kawai za su tabbatar da wadanda suka yi nasara.

Shugaban hukumar ya ce yayin da babban zaben shekarar 2023 ke gabatowa, ya zama wajibi ga masu ruwa da tsaki musamman jam’iyyun siyasa su lura da manyan abubuwan da sabuwar dokar zabe ta 2022 ta tanadar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

six − two =