Nan ba da dadewa ba ‘yan Najeriya za su fara biyan harajin kashi 12.5 cikin 100 na sadarwar wayar salula a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke shirin fara aiwatar da karin kashi 5 cikin 100 na harajin ayyukan sadarwa a Najeriya.
Ministar kudi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da harajin ayyukan sadarwa a Najeriya jiya a Abuja.
Hukumar Sadarwa ta kasa ce ta shirya taron.
Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa, za a kara kashi 5 cikin 100 na harajin akan kashi 7.5 da ake karba kan ayyukan sadarwa.
Zainab Ahmed, wacce ta samu wakilcin mataimakin babban jami’in ma’aikatar, Frank Oshanipin, ta ce karin kashi 5 cikin 100 na harajin na cikin dokar kudi ta 2020 amma ba a fara aiwatar da shi ba.
Ta ce an samu tsaikon fara aiwatar da shi ne sakamakon tattaunawar da gwamnati ke yi da masu ruwa da tsaki.