Sanatoci sun yi barazanar tsige Buhari saboda rashin tsaro

42

Sanatoci daga jam’iyyun adawa sun baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari wa’adin makonni shida da ya magance matsalar rashin tsaro a kasarnan ko kuma a tsige shi.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Philip Aduda, shine ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai bayan da ‘yan majalisar adawa suka fice daga zauren majalisar a fusace.

Rikicin dai ya faro ne a lokacin da shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan ya gabatar da batun bayar da umarni ga majalisar dattawan ta tattauna kan batutuwan da aka tabo a zaman da aka yi cikin sirri amma Ahmad Lawan ya ki amincewa.

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan bayan zaman majalisar zartarwa ya bayyana cewa an tattauna batutuwan da suka shafi ayyukan majalisar da hadin kan Najeriya inda ya bukaci shugabannin majalisar da su ci gaba da aiwatar da abubuwan da aka jera a cikin takardar dokokin aiki.

Sanatocin adawar sun fice daga zauren majalisar, suna rera wakoki, suna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan da su yi murabus.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two + seven =