Hukumar Kare Hakkin Mai Saye ta Jihar Kano, ta ce ta kwace buhuna 487 na fulawar da ta lalace ta miliyoyin Naira a jihar.
Mukaddashin Manajin Daraktan Hukumar, Baffa Babba-Dan’agundi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Kakakin Hukumar, Musbahu Yakasai ya fitar jiya a Kano.
Baffa Babba-Dan’agundi ya ce wasu mutanen kirki ne suka sanar da hukumar game da fulawar da ta lalace da aka kawo kasuwar hatsi ta kasa da kasa dake Dawanau a Kano.
Ya bayyana cewa an kwace fulawar ne, biyo bayan farmakin da aka kai a wani dakin ajiyar kaya da ke Kasuwar Dawanau a Kano, ranar Lahadi.
Baffa Babba-Dan’agundi ya kara da cewa hukumar ta kuma kwace wasu katan-katan na kayan shaye-shaye da lokacin amfaninsu ya wuce a kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi dake Sabongarin Kano.
Ya kuma bayyana cewa an kwashe fulawar da ta lalace da abubuwan shan, inda aka kai su dakin ajiya na hukumar.