Shugaban Sri Lanka ya tsere daga kasar

50

Shugaban kasar Sri Lanka, Gotabaya Rajapaksa ya tsere daga kasar a cikin wani jirgin saman soji, a daidai lokacin da ake gudanar da zanga-zanga kan matsin tattalin arziki.

Rundunar sojin saman kasar ta tabbatar da cewa shugaban kasar mai shekaru 73 da haifuwa ya tafi kasar Maldives tare da matarsa ​​da jami’an tsaro biyu.

Shugaban da iyalansa sun isa Male, babban birnin Maldives.

Guduwar Gotabaya Rajapaksa ya kawo karshen daular gidansu da ta yi mulkin Sri Lanka tsawon shekaru da dama.

Shugaban kasar ya buya bayan da jama’a suka mamaye gidansa a ranar Asabar, kuma ya yi alkawarin yin murabus a yau.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa shugaba Rajapaksa ba zai ci gaba da zama a Maldives ba kuma yana da niyyar tafiya zuwa wata kasar.

Shi ma dan uwansa, tsohon ministan kudi, Basil Rajapaksa, ya bar kasar ta Sri Lanka kuma an ce zai nufi Amurka.

Yayin da al’ummar kasar Sri Lanka suka farga da wannan labari, dubban mutane sun fito kan titunan babban birnin kasar, Colombo.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen + twenty =