Za a dauki ma’aikata miliyan 1 domin aikin kidaya

50

Hukumar kidaya ta kasa (NPC) tace gwamnatin tarayya za ta dauki jumillar ‘yan Najeriya miliyan 1 aikin kidayar jama’a na kasa da za ayi a shekarar 2023.

Hukumar ta tabbatar da cewa za ayi amfani da fasahar zamani wajen gudanar da kidayar domin hana ‘yan siyasa da wasu manya sauya alkaluman kidayar.

Kwamishinan dake wakiltar jihar Ekiti a hukumar, Deji Ajayi, shine ya sanar da haka a yau a Ado Ekiti, babban birnin jihar.

Kwamishinan ya kara da cewa an zabi garuruwa tara daga kananan hukumomi tara cikin kananan hukumomi 16 na jihar, domin gudanar da kidayar gwaji.

Da yake bayani akan muhimmancin kidayar, Deji Ajayi, yace kungiyoyi masu zaman kansu suna amfani da alkaluman kidayar wajen daukar matasa aiki bayan sanin yawan al’ummar dake ko’ina.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × 4 =