A fara yiwa masu shirin aure gwajin kwayoyi – NDLEA

64

Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, Buba Marwa, ya jaddada bukatar yin gwajin maganin miyagun kwayoyi ga masu shirin aure.

Buba Marwa ya shaida wa tawagar kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen jihar da suka ziyarce shi jiya a Yola, babban birnin Jihar, cewa ya dace iyaye su tabbatar da matakin amfani da miyagun kwayoyi na ‘ya’yansu dake shirin aure.

Ya jaddada cewa akwai bukatar tantance amfani da miyagun kwayoyi kan masu shirin aure da ‘yan siyasa, kuma a tsare wadanda aka kama suna ta’ammali da miyagun kwayoyi domin gyara musu rayuwa.

Buba Marwa ya bayyana cewa kashi 80 cikin 100 na masu shaye-shayen kwayoyi na bukatar shawarwarin da za su iya samu a cibiyoyi 26 na hukumar ta NDLEA, inda ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta amince da karin wasu cibiyoyi shida na gyaran rayuwar masu shaye-shaye.

Tun da farko, shugaban kungiyar ‘yan jaridun, Ishaka Dedan, ya yaba da gudunmawar Buba Marwa a yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi, inda ya ce an samu nasarori da dama.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 + seven =