Za a fara amfani da fasahar 5G a watan Augusta – NCC

42

Hukumar Sadarwa ta Kasa, NCC, ta ce za ta kaddamar da fasahar shiga intanet ta 5G a watan Agustan bana.

Mataimakin shugaban hukumar Farfesa Umar Dambatta ne ya bayyana haka a taron majalisar masu amfani da wayar tarho karo na 90 da aka gudanar jiya a Legas.

Umar Dambatta ya ce hukumar NCC, ta hanyar tallafin ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani ta tarayya, za ta tabbatar da fara amfani da fasahar don kara habaka ci gaban ayyukan sadarwa a kasarnan.

Ya ce bisa la’akari yawan mutanen kasarnan kimanin miliyan 214; tare da cigaban da ake samu na kashi 2.6 a kowace shekara a takaice, kimanin kashi 76.46 na yawan jama’a zasu kasance ‘yan kasa da shekaru 35.

Umar Dambatta ya nanata cewa, burin hukumar shi ne Najeriya ta kasance daya daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen amfani da fasahar 5G wadda domin amfanin masu ruwa da tsaki da kuma bayar da gudunmawa sosai ga manufofin gwamnatin tarayya kan tattalin arziki na zamani.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × five =