IPPIS ya rage yawan ma’aikata zuwa 720,000 – Gwamnati

41

Darakta-Janar na ofishin sake fasalin ma’aikatan gwamnati, Dakta Dasuki Arabi, ya ce bullo da tsarin biyan albashi na IPPIS, ya rage yawan ma’aikatan gwamnatin tarayya zuwa dubu 720.

A cewar sa, IPPIS ta tankade ma’aikatan bogi kimanin dubu 70, lamarin da ya jawo ta tarawa gwamnatin tarayya kudi sama da naira miliyan dubu 220.

Dasuki Arabi ya bayyana haka ne a jiya, yayin da yake jawabi a taron manema labarai karo na 43 da kungiyar kafafen yada labarai na fadar shugaban kasa ta shirya a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Da yake bayar da karin haske kan yadda ofishin ke gudanar da muhimman ayyukansa, musamman wajen tabbatar da aiwatar da tsare-tsare da shirye-shiryen gwamnati, Dasuki Arabi ya ce gwamnati ta kuma samu naira tiriliyan 10 bayan kaddamar da tsarin asusun ajiyar kudade na bai daya wato TSA.

Babban daraktan ya ce a wani bangare na garambawul a ayyukan gwamnati, tsarin hada-hadar kudi na zamani ya mayar da gudanar da ayyukan gwamnati ba tare da amfani da takarda ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × four =