Kotu ta hana gwamnatin Bauchi gurfanar da tsoffin gwamnoni biyu

55

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da gwamnatin jihar Bauchi daga tuhumar wasu tsoffin gwamnoni biyu bisa zargin karkatar da kudade da kadarorin jihar.

Tsoffin gwamnan su ne Isa Yuguda da Mohammed Abubakar.

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Inyang Ekwo, ya kuma soke tuhumar da kwamitin karbo kadarori da kudade na jihar da Gwamna Bala Mohammed ya kafa domin binciken magabatan sa biyu Isa Yuguda da Mohammed Abubakar.

Mai shari’a Ekwo, wanda ya bayyana kwamitin a matsayin haramtacce, ya hana gwamnatin jihar yin aiki da rahoton kwamitin domin gurfanar da su a gaban kuliya.

Kwamitin ya tuhumi tsoffin gwamnonin biyu da laifin karkatar da kadarorin jihar da kuma kudaden da suka kai naira miliyan dubu 321 da miliyan 500.

Isa Yuguda da Mohammed Abubakar sun shigar da karar ne domin kalubalantar rahoton kwamitin.

Sun yi ikirarin cewa, ba ya ga kasancewar gwamna mai ci ya kafa kwamitin bisa haramtacciyar doka, ya kuma kafa shi ne da nufin bata musu suna.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × one =