Buhari ya gayawa gwamnonin APC cewa yana so ya zabi wanda zai gaje shi

39

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shaidawa gwamnonin jam’iyyarsa ta APC cewa zai so ya zabi wanda zai gaje shi kuma yana bukatar gwamnoni su mara masa baya wajen yin hakan.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a jiya a wani taro da gwamnonin jam’iyyar APC a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaba Buhari ya shaida wa gwamnonin cewa ya fahimci bukatar samar da kwakkwaran jagoranci ga jam’iyyar a wannan hali na mika mulki.

Shugaban ya ce shugabanci mai karfi ba wai don tabbatar da nasar APC bane kadai, har ma da tabbatar da cewa jam’iyyar ta ci gaba da rike madafun iko a sama ta hanyar lashe zaben shugaban kasa.

A ganawar da gwamnonin, shugaba Buhari ya kuma bayyana abubuwan da zai yi la’akari da su wajen marawa dan takarar shugaban kasa baya a cikin mutane 23 da ke neman takarar a jam’iyyar APC.

Shugaban ya tafi kasar Sifaniya ne bayan ganawarsa da gwamnonin, inda daga bisani suka sake kiran wani taro domin tattaunawa kan bukatar shugaban kasar.

A wani batun kuma, ba a samu cimma matsaya ba a zaman ganawar da gwamnonin jam’iyyar APC suka gudanar a yammacin jiya domin tattaunawa kan bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

An gudanar da zaman ne a Abuja, mintuna kadan bayan ganawar gwamnonin APC da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A nasu zaman ganawar, daya daga cikin gwamnonin ya shaidawa manema labarai cewa gwamnonin sun kasa cimma matsaya kan yadda za a aiwatar da bukatar shugaban kasa.

Majiyar ta ce da yawa daga cikin gwamnonin Arewa, sun ce babu wani gwamnan kudu da zai iya kayar da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP; don haka a bawa dan Arewa. Sai dai hakan ya harzuka wasu gwamnonin kudu.

Wasu daga cikin gwamnonin kudancin kasarnan kuma sun ce ba dole ne wanda za a zaba ya zama gwamnan jiha ba, kuma ana kyautata zaton gwamnonin da ke biyayya ga wasu ‘yan takarar shugaban kasa a kudancin kasar irin su mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Bola Tinubu ne suka kawo wannan batun.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five − 3 =