Sarkin Musulmi ya yi Allah wa dai da kisan dalibar da ta yi batanci a Sokoto

153

Mutane dayawa sun tofa albarkacin bakinsu a jiya bayan kisan da aka yi wa Deborah Samuel, wata dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato, bisa zarginta da yin batanci.

An rawaito cewa dalibar dake matakin karatu na biyu ta yi kalaman batanci ga fiyayyen halitta a group din WhatsApp.

Gwamnatin jihar Sokoto ta mayar da martani inda ta bayar da umarnin rufe kwalejin cikin gaggawa.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar ta ce an kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan dalibar yayin da aka fara farautar sauran wadanda ake zargi da suka tsere.

A halin da ake ciki, Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa dalibar.

Sarkin, a wata sanarwa da sakataren Majalisar Sarkin Musulmi ya fitar, ya bukaci da a kamo tare da hukunta dukkan wadanda suka aikata kisan.

A wani labarin mai alaka da wannan, Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano wacce ke zama a Kofar Kudu, ta umurci Majalisar Agajin Lauyoyi ta kasa da ta samar da lauya ga Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara sakamakon korar lauyan sa Ambali Muhammad daga shari’ar batanci da ake cigaba da yi masa.

Da kotu ta tambaye shi ko zai gabatar da wani sabon lauya, malamin ya roki a bar shi shi kadai ya ci gaba da shari’ar sa saboda ba zai samu wanda zai tsaya masa ba.

Amma da suke nuna rashin amincewa, tawagar masu shigar da kara karkashin jagorancin Farfesa Nasir Adamu Aliyu ta ce idan aka yi la’akari da girman laifin da ake tuhumarsa da shi, rashin samun lauyan da zai kare shi zai yi mummunan tasiri a shari’ar.

Don haka ya roki kotun da ta bukaci majalisar ba da agajin shari’a ta ba shi lauya kamar yadda sashe na 36 na kundin tsarin mulkin kasarnan ya tanadar.

Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya amince da rokon sannan ya bukaci majalisar bayar da agajin shari’a da ta samar da lauya ga wanda ake kara.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen − 13 =