Jami’ar FUD ta zama ta daya a Afirka a fannin lissafi

78

Wata kungiyar bincike daga jami’ar Granada ta kasar Sifaniya mai suna CImago ta bayyana jami’ar tarayya dake Dutse a matsayin jami’a ta daya a nahiyar Afrika a fannin lissafi a cikin jami’o’i 422 da aka tantance.

Matsayin kungiyar na bana wanda aka bayyana kwanan nan ya kuma sanya Jami’ar Tarayya ta Dutse a matsayin na 43 a fannin kirkire-kirkire a Afirka kuma ta 55 a fannin bincike a Afirka sannan ta 66 a gaba daya a Afirka cikin jami’o’i 422.

A kididdigar jami’o’in Najeriya gaba daya da kungiyar ta yi, jami’ar ta zama jami’a ta 10 a gaba daya a Najeriya yayin da kuma ta zama na 13 a fannin bincike da kuma ta 9 a fannin kirkire-kirkire a Najeriya.

Idan za a iya tunawa dai, wasu matasa uku da suka fito daga sashen ilmin lissafi na jami’ar ne suka shiga jerin kashi biyu cikin 100 na masana kimiyyar da aka fi aiki da bincikensu a duniya.

Mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed ya taya ma’aikata da daliban jami’ar murnar wannan gagarumar nasara.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty + eleven =