NGF ta tallafawa wadanda harin jirgin kasa ya shafa

60

Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya bayyana cewa kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) za ta cigaba da bayar da goyon baya ga kokarin gwamnatin tarayya na magance matsalar rashin tsaro.

Gwamnan ya bayyana haka ne a jiya a lokacin da ya kai ziyara gidan gwamnatin jihar Kaduna domin jajantawa jihar bisa harin da aka kai kan jirgin kasa ‘yan kwanakin nan.

Idan dai za a iya tunawa mutane takwas ne suka mutu, wasu kuma suka samu raunuka yayin da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta kan wani jirgin kasa a Kaduna a ranar 28 ga watan Maris.

Da yake magana kan lamarin, Kayode Fayemi, wanda ya ziyarci jihar tare da gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, a madadin kungiyar gwamnonin Najeriya, ya ce za a yi kokarin ganin an dawo da zaman lafiya a Kaduna da sauran jihohin da ke fuskantar hare-hare.

A cewar wata sanarwa da kungiyar ta fitar, Gwamna Fayemi ya bayyana harin a matsayin abin tayar da hankali.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twelve + five =