Kotu ta kori karar dake neman hana Atiku tsayawa takarar shugaban kasa

53

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a yau, ta yi watsi da karar da aka shigar tun 2019, tana neman kalubalantar cancantar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na tsayawa takarar kujerar shugaban kasa.

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Inyang Ekwo, ya yi watsi da karar bisa hujjar cewa wanda ya shigar da karar ba shi da hurumin yin hakan.

Wata kungiya ta kai karar Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) da Atoni Janar na Tarayya.

Kungiyar dai na kalubalantar cancantar Atiku na tsayawa takarar shugaban kasa bisa hujjar cewa shi ba dan Najeriya ba ne.

A wani labarin kuma, dan takarar shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu a jiya a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ya ce babu wani cin zarafi ko tsoratarwa da zai iya hana shi neman shugabancin kasar a 2023.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci Olubadan na Ibadan, Lekan Balogun, domin neman albarkarsa kan burinsa na zama shugaban kasa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × five =