Gwamnati za ta binciki shigo da gurbataccen man fetur

47

Gwamnatin Tarayya za ta kaddamar da bincike domin bankado yadda aka shigo da gurbataccen man fetur dauke da sinadarin methanol sama da kima.

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva ne ya bayyana hakan a yau yayin da yake gabatar da tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya na mako mako wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Ministan, wanda ya ce gwamnati na taka-tsan-tsan wajen tunkarar al’amuran da suka shafi gurbataccen man fetur, ya nemi a kara hakuri domin kawo karshen binciken kafin duk wani yunkuri na bankado masu hannu a cikin lamarin.

Ya kuma ce za a yi la’akari da al’amuran da suka shafi ababan hawa da suka lalace sakamakon lamarin da ba a saba gani ba wajen tunkarar lamarin.

Timipre Sylva ya ce Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), zai iya magance halin da ake ciki a yanzu.

A wani batun kuma, majalisar zartaswa ta tarayya ta amincewa ‘yan kasashen waje su 286 su zama ‘yan Najeriya daga cikin mutane 600 da suka nemi hakan.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a yau bayan taron majalisar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

A cewarsa, adadin wadanda aka tabbatar da amincewa su zama ‘yan kasa sun kai 208, yayin da masu neman hakan su 78 aka amince da su ta hanyar rajista.

Masu neman zama ‘yan Najeriya sun fito daga kowane yanki na duniya da suka hada da Turawa da Amurkawa, da sauran su, kuma hukumomi irin su hukumar tsaro ta farin kaya DSS da ma’aikatar harkokin kasashen waje da hukumar shige da fice ta kasa immigration da kuma gwamnatocin jihoshin da mutanen suke zaune, sun gudanar da bincike sosai akan su.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × 3 =