Da safiyar ranar Talata ne a jihar Kano aka wayi gari da ziyarar jaje da ta’aziya daga mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.
Osinbajo yazo Kanon ne don jajantawa iyayen Haneefa Abubakar; wadda malaminta Abdulmalik Tanko yai wa kisan gilla.
Tini dai hukumomi a Kanon suka gurfanar da Abdulmalik a gaban kuliya tare da wasu karin mutum biyu da ake zargin suna da hannu a kisan nata.
Haneefa dai an dauke ta daga gida tsawon makonni tare da neman kudin fansa, kafin daga bisani masu garkuwar su kasheta ta hanyar bata guba.