Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta kasa ta ce ya zuwa jiya, sama da mutane miliyan 15 ne aka yiwa allurar rigakafin korona a karon farko.
Hukumar ta bayyana hakan ne a yau ta shafinta na Facebook.
A cewar hukumar, mutane miliyan 15 da dubu 110 da 459 na jimlar wadanda suka cancanta a yiwa rigakafin corona, an yi musu allurar a karon farko, yayin da mutane miliyan 5 da dubu 574 da 696 daga cikin wadanda suka cancanci allurar rigakafin, aka yi musu sau biyu.
Jihar Jigawa ce ke kan gaba, inda ta ke da mutane miliyan 1 da dubu 846 da 483 da aka yiwa rigakafin, sai jihar Legas mai mutane miliyan 1 da dubu 460 da 808 sai Kano mai mutane miliyan 1 da dubu 136 da 858.
Hukumar ta ce adadin mutanen da aka yiwa allurar rigakafin sau daya a Najeriya ya kai kashi 13.5 bisa dari na mutanen da suka cancanci rigakafin, yayin da adadin wadanda aka yi musu allurar sau biyu ya kai kashi biyar cikin 100.