Buhari ya gana da Jonathan akan rikicin Mali

16

Shugaban kasa Muhammadu Buhari jiya a Abuja ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan al’amuran siyasar da suke wakana a kasar Mali.

Goodluck Jonathan shi ne jakada na musamman na kungiyar ECOWAS a kasar Mali.

A ranar Lahadi ne kungiyar ta ECOWAS za ta gudanar da wani taro na musamman kan kasar Mali a Ghana domin tattaunawa kan halin da ake ciki a kasar.

Mai magana da yawun shugaba Buhari, Femi Adesina, ya bayyana cewa taron na ranar Lahadi shine batun ganawa tsakanin shugaban kasar da Goodluck Jonathan.

Ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya sake nanata alkawarin da ya yi a baya cewa duk abin da Najeriya za ta yi kan lamarin Mali za ta yi shi ne a karkashin kungiyar ECOWAS.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa, a jiya ne shugaba Buhari ya karbi bakuncin babban jakada na musamman na shugaban rikon kwarya na kasar Mali, Kanal Assimi Goita.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × 1 =