Osinbajo zai halarci bikin binne Mugabe

45
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo

Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo zai halarci bikin binne tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe da za’ayi yau Asabar a babban birnin kasar.

Osinbajo zai wakilci shugaban kasa Muhammdu Buhari ne wanda yake halartar taron shugabannin kasashen yammacin Afrika a Burkina Faso, inda zasuyi wata ganawa a yau Asabar don sabunta dabarun yaki da ta’addanci a kasashen yammacin sahel.

Andai yi takaddama a baya kan inda ya dace a binne Mugabe, inda iyalansa sukaso a gina masa katafaren daki a mahaifarsa kuma a binne sa a ciki, amma hakan bai yiwu ba.

Yanzu dai an cimma matsaya inda aka amince a binne tshohon shugaban kasar da ya jagoranceta na tsawon shekaru 37 a wata makarbata da ake binne gwarzayen kasar.

Isowar gawar Mugabe Zimbabwe

A bikin binne Mugabe da za’ayi yau, ana sa ran shugabannin kasashen Afrika na da, da na yanzu kusan 20 zasu halarci bikin.

Osinbajo da sauran mukarraban gwamnati da zasu halarci bikin ana sa ran zasu dawo Abuja yau da zaran an kammala binne Mugabe.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

6 − two =