Yansanda na binciken kalaman kiyayya ga Musulmai a India

19

Bidiyon da ke nuna shugabannin addinin Hindu a Indiya suna kira da a yi wa musulmai kisan kiyashi ya haifar da fushi tare da neman daukar mataki.

‘Yan sandan Indiya a yau sun ce sun kaddamar da binciken kalaman nuna kiyayya a kan lamarin da ya faru a Haridwar da ke arewacin jihar Uttarakhand a makon da ya gabata, inda mahalarta taron suka yi kira da a yi kisan gilla da kuma amfani da makamai kan musulmai.

A cewar wani faifan bidiyo da ake yadawa, wani mai jawabi a wurin taron ya shaida wa mahalarta taron cewa kada mutane su damu da batun shiga gidan yari saboda kashe musulmai.

Taron ya samu halartar akalla memba daya na jam’iyyar BJP ta Firayim Minista Narendra Modi.

Ana zargin jam’iyyar da karfafa muzgunawa musulmi da wasu marasa rinjaye daga masu tsatsauran ra’ayin addinin Hindu, tun bayan hawanta karagar mulki a shekara ta 2014, zargin da ta musanta.

Gwamnatin Narendra Modi ba ta ce komai ba game da taron.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × five =