Gwamnatin Tarayya ta ayyana hawa jirgin kasa a kyauta

19

A yau ne gwamnatin tarayya ta ayyana aiyukan sufurin jiragen kasa a kyauta a fadin kasar nan.

Kakakin Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Kasa, Mahmood Yakub, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ‘yan Najeriya za su iya more hawa jiragen kasa a kyauta tsakanin ranar 24 ga watan Disamba zuwa 4 ga watan Janairu.

Ya ce hawa jiragen a kyauta ya shafi dukkan hanyoyin jiragen kasa na kasarnan.

Hanyoyin sun hada da titin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna, da na Legas zuwa Ibadan, da Warri zuwa Itakpe, da Kano zuwa Lagos, da Minna zuwa Kaduna da kuma Aba zuwa Fatakwal.

Manajan Daraktan Hukumar Jiragen Kasa ta kasa, Engr. Fidet Okhiria, wanda shi ma ya yi magana game da karamcin, ya ce an dauki matakin ne tare da hadin gwiwar ma’aikatar sufuri, da nufin saukake zirga-zirgar ‘yan kasa a lokacin bukukuwan karshen shekara.

Ya kuma nanata kudurin gwamnatin tarayya na tabbatar da tsaron lafiyar fasinjoji da jiragen kasa a wannan lokacin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 − 2 =