Gwamnatin Jigawa ta kashe sama da N1.4bn akan Corona

3

Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe kudi fiye da naira miliyan dubu daya da miliyan 438 wajen sayen kayayyakin rage radadin cutar corona da kuma bayar da kwangila ga kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa a jihar nan a shekarar da ta gabata.

Wakilin ma’aikatar kudi ta jiha Alhaji Haruna Danlami ya bayyana hakan a kasidar da ya gabatar a taron fadakar da kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa hanyoyin samun kwangila a saukake domin rage karayar tattalin arziki da annobar corona ta haifar, wanda gwamnatin jiha ta shirya a Maimuna Millenium Park, Hadejia

Yace akasarin ma’aikatu da hukumomin gwamnati na da rarar kudade da zasu aiwatar da kashi na biyu na shirin gwamnati na tallafawa kananan ‘yan kasuwa da bayar da kananan kwangiloli.

A jawabinsa, kwamishinan ilmi, kimiyya da fasaha na jiha, Dr Lawan Yunusa Danzomo, yace ma’aikatarsa zata baiwa kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa guda 200 kwangiolin sayowa da samar da kayayyakin koyo da koyarwa, nan da karshen wannan shekara.

A wani labarin kuma, kwamitin kare hakkin mai saye da sayarwa na jihar Jigawa ya samu nasarar kama wasu mutane hudu a kasuwar Hadejia bisa laifin cakuda kasa da ruwa a bahu 37 na kanwa.

Shugaban kwamitin Alhaji Farouk Abdallah Mallam Madori ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

Yace an samu mutanen ne da laifin cakuda kasa da ruwa da garin kanwa suna shanyawa sannan in ya bushe su zuba a buhu su kai kasuwa.

Alhaji Farouk Abdallah ya ce tuni suka mika su gaban kotun tafi da gidanka domin su girbi abin da suka shuka.

Kotun ta aike su zuwa gidan gyaran tarbiyya na mako guda, bayan sun yi sati guda an dawo dasu kotun ta daure su na tsawon watanni goma goma ko zabin biyan tarar kudi naira dubu tamanin kowannensu tare da kwace buhunan kanwar gaba daya.

Mutanen sun hadar da Kawu Muhammad da Babangida Muhammad da Usman Muhammad da Danladi Mai Kanwa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 + thirteen =