Gwamnatin Tarayya ta kashe N2.3trn a matsayin tallafin corona

20

Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Kasa, Clement Agba, ya ce gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta kashe naira tiriliyan 2 da miliyan 300 a matsayin tallafi don dakile illar annobar COVID-19 a kasarnan.

Clement Agba ya bayyana haka ne jiya a wajen wani taron karawa juna sani na kwana uku karo wanda ofishin Akanta Janar na kasa ya shirya a Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom.

Ya ce wadannan tallafin sun samar da guraben ayyukan yi da dama, sun samar da jari ga manoma da ’yan kasuwa, sun tanadi kudaden musaya na kasashen waje da samar da kayan amfanin gona, musamman a fannin noma da gidaje.

Ministan ya kara da cewa duk da kalubalen corona, har yanzu Najeriya ce kasa mafi karfin tattalin arziki kuma mafi yawan jama’a a nahiyar Afirka.

Clement Agba ya ce gwamnatin tarayya za ta cigaba da samar da yanayin da zai bunkasa harkokin kasuwanci a kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 − 7 =