Gwamnatin Tarayya ta raba kudaden UBEC ga makarantu 1,147

22

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da rabon kudade ga makarantu dubu 1 da 147 karkashin asusun hukumar ilimin bai daya domin inganta ilimin bai daya a kasarnan.

Ministan ilimi, Adamu Adamu, ya sanar da haka jiya a Gombe yayin kaddamar da shirin rabon kudaden na asusun tallafawa na hukumar ilimin bai daya.

Ministan wanda ya samu wakilcin karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, yace shirin na tallafawa al’umma wanda masu ruwa da tsaki zasu gudanar, da yake bukatar hadin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki domin aiwatar da shi cikin nasara.

Tunda farko, babban sakataren hukumar ilimin bai daya, Dr Hamid Bobboyi, yace taron na tattaunawa da al’umma, an gudanar da shi da nufin samar da wani tsari mai kyau domin samar da ilimin bai daya a kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

7 + 12 =