Gwamnatin Jigawa za ta wayar da kai akan kudaden shiga

41

Jami’an Gwamnatin jihar Jigawa za su ziyarci kasuwanni da kauyuka domin wayar da kan al’umma muhimmancin bayar da kudaden shiga.

Wakili a kungiyar tabbatar da adalci kan karbar kudaden shiga Dr Sa’id Umar shine ya bayyana hakan ta cikin wani shirin radio Jigawa.

Sa’id Umar wanda ya gabatar da kasida a taron farko da gwamnatin jihar Jigawa ta gudanar kan muhimmancin karbar kudaden shiga, ya bayyana muhimmancin da karbar kudaden shiga yake dashi ga kowacce gwamnati.

Yace ‘yan kasuwa da talakawa da ma’aikata suna biyan kudaden shiga domin kara bai wa gwamnati dama wajen gudanar da muhimman ayyukan raya kasa.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar tuntuba kan kudaden shiga na jiha, Muhammad Abdu Dutse, yace suna bibiyar kudaden shiga da gwamnati ta tara domin amfanin al’umma.

A jawabinsa, shugaban kungiyoyin kyautatuwar zaman jama’a na jihar Jigawa, Comrade Musbahu Basirka yace biyan kudaden shiga yana tabbatar da bin doka da oda inda yace kungiyoyi zasu cigaba da wayar da kan al’umma muhimmancin bayar da kudaden shiga domin inganta rayuwa da zamantakewa.

A wani labarin kuma, majalisar dokokin jihar Jigawa ta yi gyara a dokar oditoci ta jiha da kuma kara wasu sassa a cikin dokar.

Gyaran dokar da kuma kara wasu sassa ya biyo bayan wasikar da Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya aikewa majalisar wadda ke bukatar yin gyaran.

A lokacin zaman shugaban majalisar, Alhaji Idris Garba Jahun ya ce gyaran dokar zai samar da karin iko ga babban mai binciken kudi na jiha da na kananan hukumomi kan batun da ya shafi kasafin kudi da kashe kudi da kuma bunkasa kwazon ma’aikata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 − 5 =