
A jiya Laraba da misalin karfe 9:30 na dare ne jirgin farko da ya kwaso ‘yan Nijeriya ya sauka a babban filin tashi da saukan jiragen sama na birnin Legas.
Tun bayan dai rikicin nuna kin jinin baki da al’ummar Afrika ta Kudu ke nuna wa ‘yan kasashen waje da akayi kwanakin baya, kamfanin jiragen Air Peace yasha alwashin kwaso ‘yan Nijeriya da ke bukatar dawowa gida kyauta.
‘Yan Nijeriya da suka iso jiya sun samu tarban manyan jami’an gwamnati, shugaban kamfanin jiragen Air Peace da kuma shugabar hukumar ‘yan Nijeriya mazauna ketare Abike Dabiri, inda ta bayyana cewa gwamnatin zata tallafawa wadanda suka dawo din domin ganin sun samu abun yi.