‘Yansanda sun kama mutane 4 da ake zargi da garkuwa da mutane a Jigawa

78
Gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, a jiya, ta ce ta cafke wasu mutane hudu na gungun barayin da suka kware wajen satar mutane a sassa daban-daban na jiharnan.

Mai magana da yawun rundunar, Lawal Shiisu Adam, a cikin wata sanarwa a jiya, ya ce kamen ya biyo bayan korafin jama’a kan manyan laifukan garkuwa da mutane a jihar.

Wanda ake zargi na farko da aka kama, wani mutum ne mai shekara 40 dan asalin rigar Fulani ta Gidan Maza da ke Karamar Hukumar Garki, wanda ya yi ikirarin cewa shi da wasu gungun mutane 9 na da hannu a sace wani dan kabilar Igbo da wani Bahaushe.

Wanda ake tuhuma na biyu ya furta cewa ya fara da satar dabbobin gida kafin ya shiga fashi da makami da garkuwa da mutane shekaru uku da suka gabata. Yayin da wacce ake zargi ta uku ta kasance matar aure ce ga wanda ake zargi na biyu.

Shiisu Adam ya bayyana cewa binciken ‘yan sanda ya kuma kai ga cafke mutane na hudu da ake zargi a Gora Arewa dake Chai-Chai a karamar hukumar Ringim wanda ya yi ikirarin yana karbar baburan da aka sace yana sayar da su a kasuwannin Gujungu da Shuwarin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twelve − eight =