Gwamnatin Tarayya ta soke hukumomin DPR, PPPRA da PEF

28
Muhammadu Buhari

Gwamnatin tarayya ta ce ta soke hukumomi uku a bangaren mai kamar yadda sabuwar dokar man fetur ta tanada.

Dokar, wadda aka sa hannu a kanta a watan Agusta ta bukaci a soke hukumomin DPR da PPPRA da PEF.

An kafa wasu sabbin hukumomi biyu masu lakabin NPRA da NURC wadanda za su maye gurbinsu kuma hukumomin biyu za su sa ido ne kan hakar mai da sarrafa shi a kasarnan.

Karamin ministan harkokin man fetur, Timipre Sylva ya tabbatar da kafa sabbin hukumomin da fara aikinsu.

Timipre Sylva ya kaddamar da hukumar daraktocin sabbin hukumomin jiya a Abuja.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta kare ayyukan ma’aikatan tsoffin hukumomin uku da aka soke duk da cewa an sallami shugabanninsu daga mukamansu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × 3 =