Za a tura ‘yansanda 34,587 domin zaben Anambra

87

Babban Sufeton ‘yan sandan, Usman Alkali Baba, yau a Abuja ya ce za a tura jami’an ‘yansanda dubu 34 da 587 zuwa jihar Anambra domin zaben gwamnan jihar da za a yi ranar 6 ga watan Nuwamba.

Usman Baba ya bayyana hakan a wani taro tare da jami’an ‘yan sanda daga mukamin kwamishina zuwa sama.

Ya ce ‘yan sandan da za a tura, zasu kunshi jami’an ‘yan sanda na yau da kullum da na rundunar ‘yan sanda da na sashin yaki da ta’addanci, da na runduna ta musamman da na sashin hada bama-bamai, da na ofishin leken asiri na rundunar, da ‘yansandan kasa da kasa, INTERPOL, da na sashin kariya na musamman da tawagar likitoci.

Ya ce za a tura jirage masu saukar ungulu guda uku don sa ido ta sama yayin da kuma za a tura rundunonin ‘yan sanda na ruwa don tabbatar da tsaro da gudanar da amintaccen zabe.

Usman Baba ya ce tura rundunonin ya biyo bayan sakamakon binciken barazanar tsaro da hukumar leken asirin ta gudanar.

A wani labarin kuma, kotun koli a yau ta tabbatar da Charles Soludo a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APGA, gabanin zabe mai zuwa a jihar Anambra.

Kotun mai alkalai biyar karkashin jagorancin Mary Odili ta kuma tabbatar da Victor Oye a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.

Hukuncin kotun kolin ya tabbatar da hukuncin farko na kotun daukaka kara na jihar Kano, wanda ya tabbatar da zaben farko wanda ya samar da Charles Soludo a matsayin dan takarar jam’iyyar gabanin zaben 6 ga Nuwamban gobe.

Kotun daukaka kara ta soke hukuncin Babbar Kotun Jihar Jigawa da ta amince da zaben fidda gwani da aka gudanar wanda bangaren Jude Okeke na jam’iyyar ta APGA ya gudanar.

Charles Soludo, farfesa kuma tsohon gwamnan babban bankin kasa, CBN, shine ya lashe zaben fidda gwani na tsagin jam’iyyar APGA mai biyayya ga gwamna Willie Obiano kuma Victor Oye ne ke jagorantar tsagin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × 1 =