Gwamnatin Jigawa ta kashe sama da naira biliyan 22 wajen samar da ruwa

29

Akalla kudi naira miliyan dubu 22 aka kashe zuwa yanzu wajen aiwatar da ayyuka daban-daban na samar da ruwan sha a fadin Kananan Hukumomi 27 na jihar Jigawa.

Kwamishinan albarkatun ruwa na jiha, Ibrahim Garba Hannun Giwa, ya sanar da haka a jiya lokacin da yake mayar da martani ga manema labarai yayin taron yan jarida da kungiyar wakilan gidajen jaridu ta shirya a cibiyar Manpower dake Dutse.

Hannun Giwa ya bayyana cewa an kashe naira miliyan dubu 22 a ayyukan ruwan sha tun bayan zuwan gwamnati mai ci ta Gwamna Muhammad Badaru Abubakar.

A cewarsa, shekaru 6 baya kafin zuwan gwamnati mai ci, kashi 40 cikin 100 ne kacal na gidajen samar da ruwan sha a jiharnan suke aiki.

Ya sanar da cewa gwamnatin jihar tana asarar sama da naira miliyan 100 kowace shekara sanadiyyar lalata kayayyakin sama da ruwan sha a fadin jiharnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one + three =