Akalla mutane 20 sun mutu a girgizar kasa a Pakistan

26

Akalla mutane 20 ne suka mutu yayin da sama da 200 suka jikkata bayan girgizar kasar da ta afku a lardin Balochistan da ke kudu maso yammacin kasar Pakistan.

Kamar yadda yazo a bayanan binciken yanayin kasa na Amurka, girgizar kasa mai karfin maki 5.9 ta afku yayin da yawancin mazauna gundumar Harnai, mai nisan kilomita 100 gabas da Quetta babban birnin lardin, suke bacci da misalin karfe 3 na daren yau.

Girgizar kasar ta afku a zurfin kusan kilomita 20 kuma hukumar kula da annoba ta lardin ta ce akalla mutane 200 sun ji rauni.

Hukumar ta ce ana cigaba da binciken lalacewar gidaje da sauran gine-gine a gundumar Harnai.

Fira-Ministan Pakistan Imran Khan ya ce ya bayar da umarnin agajin gaggawa cikin gaggawa ga mazauna yankin bayan girgizar kasar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × 5 =