Buhari ya gabatar da kasafin kudin N16trn ga majalisa domin badi

14

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin badi ga zaman hadin gwiwa na majalisun kasa.

An yi kasafin kididdigar kudaden da za a kashe a badi akan naira triliyan 16 da miliyan dubu 390, inda aka kayyade farashin danyen mai akan dala 57 kowace ganga, tare da hasashen hako ganga miliyan 1 da dubu 800 a kowace rana.

An kuma yi hasashen farashin dala daya akan naira 410 da kobo 15, tare da hasashen cigaban GDP da kashi 4.2 cikin 100 da kuma hauhawara farashin kayan masarufi da kashi 13 cikin 100.

Shugaban Kasar yace an yi kiyasin jumillar kudaden shigar da ake sa ran tarawa akan naira tiriliyan 12 da miliyan dubu 720 a badi, yayin da aka yi kiyasin kudaden da za a iya samu a hannu domin kasafin kudin akan naira triliyan 10 da miliyan dubu 130.

Shugaban kasar ya nemi karin kudaden kasafin kudin daga naira tiriliyan 13 zuwa naira tiriliyan 16 da miliyan dubu 450.

Wasu hujjoji da ya bayar na karin sun hada da naira miliyan dubu 100 da za a ba wa hukumar zabe ta INEC domin shirin zaben 2023, da naira miliyan dubu 50 ga ma’aikatan lafiya a matsayin alawus-alawus, da sauransu.

A wani batun kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kare matakin gwanatinsa na yawan ciyo basussuka, inda yace har yanzu yawan bashin da ake bin kasarnan bai ta’azzara ba.

Ya fadi haka a yau yayin gabatar da kasafin kudin badi a gaban zaman hadin gwiwa na majalisun kasarnan.

Yace duk da kasancewar ‘yan Najeriya na da hujjar bayyana damuwa dangane da yawan ciyo basussukan da gwamnati ke yi, amma ya kafe kan cewa akwai bukatar ciyo basussukan kasancewar suna taimakawa wajen fitar da kasarnan daga kangin koma bayan tattalin arziki tare da habaka tattalin arzikin kasa.

Shugaban kasar yace manufar gwamnatinsa ita ce habaka cigaban kiddigar abinda kasarnan ke samarwa a shekara wato GDP daga kashi kashi 8 cikin 100 da ake da shi a yanzu zuwa kashi 15 cikin 100 kafin shekarar 2025.

Shugaba Buhari yace an tsara kasafin kudin bana akan cigaban da aka samu a kasafin kudin shekarun da suka gabata, tare da nufin cimma jadawalin cigaba na shekarun 2021 zuwa 2025.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × 3 =