Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ake zargin gwamnatinsa da murkushe ‘yancin fadin albarkacin baki, ya zargi kafafen yada labaran Najeriya da yada kalamai marasa kan gado.
Shugaban kasar ya fadi haka ne yau yayin watsa jawabinsa ta gidan talabijin don murnar cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yancin kai.
Sukar da Shugaba Buhari ya yiwa kafafen yada labarai a wani bangare na jawabinsa, ya dogara kan yadda wasu kalamai da ake yi a kafafen yada labarai ke haifar da tashe-tashen hankula.
Sai dai, yayin da Shugaba Buhari ke sukar kafafen yada labarai, ya yabawa da dimbin shugabannin Gargajiya da na Addini da Al’umma gami da sauran ‘yan Najeriya masu kyakyawan manufa, wadanda a fannonin su daban-daban suke yada sakon zaman lafiya cikin lumana.
A halin da ake ciki, Shugaba Buhari ya bayyana cewa hauhawar farashin kayan abinci a kasarnan na faruwa ne sanadiyyar ‘yan kasuwa da ke saye da boye kayan abincin.
Kalaman na shugaban kasar na zuwa ne yayin da farashin kayan abinci a Najeriya ya tashi da kusan kashi 98.85 da 99.9 cikin 100 a bara.