Gwamnatin Jigawa ta bayar da kwangilar tituna da asibiti

124

Majalisar zartarwar jihar Jigawa ta amince da sakin kudi naira biliyan 5 da miliyan 751 domin gina tituna da asibiti a wasu sassan jihar.

Kwamishinan labarai, matasa, wasanni da al’adu, Bala Ibrahim Mamsa, ya sanar da haka lokacin da yake jawabi ga manema labarai dangane da sakamakon zaman majalisar.

Yace majalisar ta amince da kudi naira miliyan 282 da dubu 600 domin gina sashe na biyu na babban asibitin garin Guri a karamar hukumar Guri ta jihar.

Kwamishinan ya kara da cewa majalisar ta kuma amince da bayar da kwangilar gina titi mai nisan kilomita 23 da rabi daga garin Ringim zuwa garin Doko, wanda ya hada kananan hukumomin Ringim da Garki na jihar, akan kudi naira biliyan 3 da miliyan 540.

Kwamishinan ya nanata jajircewar gwamnatin jihar wajen tabbatar da fitar da isassun kudi domin kammala ayyukan akan lokaci.

Bala Ibrahim ya tabbatarwa da mutanen jihar Jigawa jajircewar gwamnatin Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar wajen tabbatar da samar da ababen more rayuwa domin inganta walwala da tattalin arzikin mutanen jihar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × three =