An tsaurara matakn tsaro a harabar kotun daukaka kara da ke Abuja yayin da ake jiran dakon yanke hukunci kan karar da jam’iyar PDP da dan takaranta Atiku Abubkar suka shigar inda suke kalubalantar nasarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu a zaben da akayi cikin watan Fabarairu na wannan shekarar.
An samar da jami’an yan sanda da na fararen kaya a ciki da wajen kotun domin tabbatar da tsaro yayin shari’ar da za’ayi a yau. A kowane lokaci da ga yanzu, kowa zai san matsayinsa tsakanin Atiku Abubakar da Muhammadu Buhari.
Tun ajiya bayan kotun ta bayyana cewa yau Laraba zata yanke hukunci ake samun cece-kuce tsakanin magaoya bayan Atiku da Buhari kan yadda kowa ke ganin zata kaya a kotun.