Gwamnan Filato ya sake kakaba dokar hana fita gabadaya a Jos

65

Gwamnatin Jihar Filato ta sake saka dokar hana fita kwatakwata a Karamar Hukumar Jos ta Arewa, bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a Jihar.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Dr Makut Macham, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar yau.

Matakin na zuwa ne bayan wasu mahara sun far wa kauyen Yelwa Zangam da ke gundumar Zangam ta jihar, inda suka kashe kusan mutane 30, kodayake hukumomi ba su bayyana adadin mutanen ba.

A cewar Gwamna Simon Lalong, dokar hana fitar ta awa 24 za ta fara aiki ne daga karfe 4 na yammacin yau, 25 ga watan Agusta har zuwa sanarwa ta gaba.

Kusan mako biyu kenan da wasu mutane suka tare wa matafiya Musulmai hanya a Rukuba da ke birnin na Jos, inda suka kashe mutane 27 tare da raunata wasu da dama.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 − 10 =