Sabon Shugaban Zambia Hakainde Hichilema ya kama aiki

31

Sabon Shugaban Kasar Zambia Hakainde Hichilema ya sha rantsuwar kama aiki a gaban dubban magoya baya da suka taru a Filin Wasa na Heroes da ke Lusaka babban birnin kasar.

Mataimakiyarsa Mutale Nalumango ta zama mace ta farko da ta riƙe mukamin a Zambia.

Sabon shugaban wanda ya yi nasara kan dan hamayya Edgar Lungu da karamin rinjaye a watan da ya gabata, ya ce dole rayuwarsu ta gaba ta fuskanci kalubale amma ya ce za su farfado da tattalin arziki.

Ya yi wa ‘yan Zambia alkawarin samar da ingantaccen abinci a kowace rana. Inda yace babu wani dan Zambia da ya kamata ya kwana da yunwa.

Ya ce yana da mahimmanci a nemi sanya hannun jari a cikin kasa kafin neman tallafin kasashen yamma.

Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta duba sauye-sauye a bangaren ma’adinai da makamashi da yawon bude ido.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − thirteen =