Gwamnatin Kano ta hada kai da Faransa domin bunkasa noma

69

Gwamnatin Jihar Kano za ta kulla yarjejeniya da kasar Faransa domin habaka harkokin noma a jihar.

Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya bayyana hakan yayin da yake karbar bakuncin jakadan Faransa a Najeriya, Jérôme Pasquier, jiya a Kano.

Ganduje wanda mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta, ya ce hadin gwiwar za ta samar da sabbin hanyoyin bunkasa tattalin arzikin Kano.

Gwamnan ya godewa Faransa bisa kaddamar da aikin tituna a kauyuka sannan ya bukaci masu zuba jari da su nemi arziki a Kano ta hanyar cin gajiyar albarkatun da ke jihar.

Gwamnan ya kuma nanata jajircewar gwamnatinsa wajen dorewar danganta a bangaren ilimi da samar da ruwan sha.

Tunda farko, da yake jawabi, jakadan na kasar Faransa yace ya je Kano ne domin karfafa alaka tsakanin Najeriya da Faransa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 + eighteen =